Ministar harkokin kasuwancin kasar Turkiyya Ruhsar Pekcan ta tattauna da kwamishinan kasuwanci na Tarayyar Turai Paolo Gentilioni.
Pekcan ta yada a shafinta ta twitter cewa "mun tattauna da Gentiloni gabanin taron kolin Tarayyar Turai a kan abubuwa masu muhinmanci."
Minista Pekcan ta kara da cewa a tattaunawar sun tabo harkokin kasuwanci, tattalin arziki, harkokin kwastam da wasu dokoki tsakanin kasashen biyu.
Ta kuma jaddada cewa "Tare da Gentiloni za mu inganta harkokin kwastam ta sabunta aiyuka, za mu ci gaba da inganta hulda" inda ta mika sakon gaisuwa zuwa ga kwamishinan akan fahimtar juna da suka yi.