Ministar Harkokin Kasuwancin Turkiyya, Ruhsar Pekcan ta bayyana cewa ta gudanar da muhimmiyar taro inda ta tattauna da wakiliyar Kasuwancin Amurka Katherine Tai.
Minista Pekcan ta fitar da wata sanarwa ta shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan duniya da na bangarorin biyu ta hanyar sadarwar bidiyo da Tai.
"Mun kimanta dangantakarmu ta kasuwanci da tattalin arziki a yanzu kuma mun nuna kyakkyawar niyya don bunkasa kasuwanci tsakanin kasashenmu. Mun tattauna kan sabbin matakan da za a dauka don kara saukaka kasuwanci tsakanin kasashenmu da kuma kara yawan cinikayyar da ke tsakaninmu."