Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri'ar amincewa don yin kira ga Amurka da ta kawo karshen takunkuman shekaru 61 da ta kakabawa Kyuba.
A jefa kuri'a karo n 29 da aka yi a Babban Zauren Majalisar, kasashe mambobin MDD 184 daga cikin 193 ne suka nemi Amurka da ta janyewa Kyuba takunkuman.
Amurka da Isra'ila sun ce a'a, inda Hadaddiyar Daular Larabawa, Kwalambiya da Yukren kuma ba su jefa kuri'ar ba.
Duk da Babban Zauren na Majalisar Dinkin Duniya na da karfin fada a ji da nuna ra'ayin duniya, amma ba shi da ikon saka takunkumi ga wata kasa.
Tun ranar 19 ga Oktoban 1960 Amurka ta kakabawa Kyuba takunkuman tattalin arziki, sha'anin kudi da kasuwanci wanda shi ne takunkumin zamani mafi tsayi a tarihi.