Masar ta rage kudin diyyar da take nema daga kamfanin Ever Given

Masar ta rage kudin diyyar da take nema daga kamfanin Ever Given

Masar ta rage yawan kudin diyya daga dala miliyan 916 zuwa miliyan 550 da take nema daga wajen kamfann jirgin ruwan da ya toshe hanyar Mashigar Teku ta Suwaish.

Shugaban Hukumar Kula da Suwaish Usama Rebi ya sanar da cewa, sun rage yawan diyyar da suke bukata daga kamfanin jirgin ruwa na Ever Given don rage radadin asarar da jirgin ya janyo zuwa dala miliyan 550.

Sanarwar da aka fitar daga Hukumar ta ce, Rebi ya gana da jami'an Teku na Panama a garin Isma'iliyya na kasar Masar.

Rebi ya kuma ce, Hukumar ta yi aiki tukuru wajen kubutar da jirgin ruwan tare da hana mummunan abu afkuwa.

Jami'in ya ci gaba da cewa, a lokacin da jirgin ruwan Ever Given zai wuce bai bayyana yana dauke da abubuwan da za su iya fashewa wuta ta kama ba kuma, "Mutum 1 ya mutu, daya daga cikin injinan ceto ya dilmiye a ruwan, jiragen ruwa 48 sun sauya hanya sakamakon toshe Mashigar Suwaish da Ever Given ya yi, jiragen ruwa 15 da ma'aikata masu kunna nutso da dama ne suka yi aiki a wajen."

Rebi ya kuma tunatar da cewa, wannan batu yana gaban Shari'a, kuma suna ci gaba da tattaunawa don cimma matsaya da kamfanin jirgin ruwan.

Haka zalika sun rage yawan diyyar da suke bukata daga dala miliyan 916 zuwa dala miliyan 550.

A karar da aka shigar gaban kotun Masar, an bukaci kamfanin da ya biya Maar dala miliyan 916.


News Source:   ()