Gwamnatin Masar ta sanar da cewa, sai an biya ta diyya sannan za ta saki jirgin ruwa na dakon kaya mai suna The Ever Given' da ya toshe Mashigar Ruwa ta Suwaish tsawon kwanaki 6 sakamakon hatsarin da ya yi a watan da ya gabata.
Shugaban Hukumar da ke Kula da Mashigar Teku ta Suwaish Usama Rabii ya shaida cewa, an kammala nazari kan na'urar nadar bayanai ta jirgin ruwan da ya yi hatsari a Mashigar Suwaish.
Rabii ya ce, akwai yiwuwar matsalar inji ce ta janyo hatsarin jirgin ruwan, kuma idan masu jirgin ruwan suka yi watsi da bukatar su biya diyyar asarar da ya janyo a yankin, to za su tafi kotu, haka zalika ba za su saki jirgin ruwan ba har sai an biya su diyya.
Rabii ya kara da cewa, ana ci gaba da lissafin asarar da jirgin na 'The Ever Given' ya janyo, kuma asarar za ta iya kaiwa ta dala biliyan 1.
A ranar 26 ga Maris ne jirgin ruwan dakon kaya na 'The Ever Given' ya daki gabar teku tare da toshe Mashigar Teku ta Suwaish wanda hakan ya janyo cinkoson jiragen ruwa da dama a yankin.
Bayan aiyukan kwanaki 6 an samu nasarar janye jirgin ruwan inda aka bude babbar hanyar ta teku.