Masar da Itopiya na ci gaba da takaddama kan madatsar ruwa ta Hedasi

Masar da Itopiya na ci gaba da takaddama kan madatsar ruwa ta Hedasi

Ministan Albarkatun Ruwa na Masar Muhammad Abdulati ya sanar da cewa, ba za su amince da matakin gina madatsar ruwa a kogin Nil da Itopiya ta dauka ita kadai ta yi ba.

Labaran da jaridun Masar suka fitar sun ce, Abdulati ya fitar da rubutacciyar sanarwa albarkacin zagayowar Ranar Ruwa ta Duniya.

Abdulati ya shaida cewa, wannan madatsar ruwa ta Hedasi da Itopiya ta gina a kogin Nil, ta zama babbar matsalar da ke fuskantar Masar a yau.

Ya ce, "Masar ba za ta amince da yadda Itopiya ita kadai ta gina madatsar ruwan da kula da madatsar ita kadai ba, ba za mu amince da wannan matsala da za a haddasa mana ba."

 


News Source:   ()