Samar da kayayyaki a masana'antun Turkiyya ya hauhawa da kaso 16,6.
Hukumar Kididdiga ta Turkiyya ta fitar da sakamakon samar da kayayyaki a watan Maris a Turkiyya.
Sakamakon ya bayyana cewa, samar da kayayyaki watan Maris din 2021 ya karu da kaso 16,6 idan aka kwatanta da na watan Maris din 2020.
Ministan Masana'antu da Fasahar Kere-Kere na Turkiyya Mustafa Varank ya shaida cewa,
"Masana'antunmu sun nuna habaka da sauyi a watan Maris. Samar da kayayyaki a masana'antu ya habaka a tsawon watanni 11 a jere. A watanni 3 na farkon 2021 an samu habaka da kaso 12,3 idan aka kwatanta da na shekarar 2020. A tsakanin kasashen G20, Turkiyya ce ta fi kowacce kasa habaka a bangaren masana'antu."