Masana'antar saka ta fitar da kayayyaki dala biliyan 8.2 daga Turkiyya

Masana'antar saka ta fitar da kayayyaki dala biliyan 8.2 daga Turkiyya

Masana'antar sakar kasar Turkiyya ta  fitar da tufafi na dala biliyan 8.2 daga watan Janairu - Agusta na shekarar bana.

Dangane da bayanin da kungiyar masu fitar da kayan saka da kayan masarufi na Istanbul (ITHIB) suka yi, masana'antar saka ta Turkiyya na ci gaba da samun ci gaba a fitar da kayayyaki. 
Bangaren ya gano fitar da dala biliyan 8.2 a cikin watanni takwas na shekarar bana.

A watan da ya gabata, masana'antar masaku ta Turkiyya ta samu dala biliyan 1 na fitar da kaya tare da karuwar kashi 36 idan aka kwatanta da wannan watan na 2020, wanda ya kai adadi mafi girma na fitarwa a watan Agusta.


News Source:   ()