Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da daina sayarwa Saudiyya da HDL makamai

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da  daina sayarwa Saudiyya da HDL makamai

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira ga kasashe mambobin Tarayyar da su daina sayarwa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa makamai saboda yadda suke take hakkokin dan adam a Yaman.

A wani kudirin doka da aka gabatar a majalisar mai taken "Yanayin Siyasa da Mutane a Yaman", an tunatar da cewa, a baya ma an taba yin kiran da a dakatar da sayarwa Saudiyya duk wani nau'i na makami.

Kudirin ya bayyana yadda Jamus ta daina sayarwa da Saudiyya makamai da yadda Italiya ta da dakatar da sayarwa Saudiyya da Hadaddiyar Daukar Larabawa makaman, amma har yanzu wasu kasashen Turai na ci gaba da sayar musu wanda hakan ya sabawa dabi'un kawancen.

Kudirin ya bayyana gamsuwar Tarayyar Turai kan yadda Amurka ta dakatar da sayarwa Saudiyya makamai da kuma fasa bawa Hadaddiyar Daular Larabawa jirgin yaki samfurin F-35.

'Yan majalisar na Tarayyar Turai sun ce, fitar da makamai da kasashen Tarayyar ke yi na kara rura wutar rikicin Yaman.

A baya-bayan nan an gano yadda a Yaman, aka yi amfani da makaman da Saudiyya ta saya daga yankin Valon na Beijiyom.

Haka zalika Ostireliya ta sanar da ba za ta daina sayar da makamai ga Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da ke goyon bayan wani bangare a rikicin na Yaman ba.


News Source:   ()