Majalisar Dinkin Duniya kafin a fara gudanar da taron Siriya a Brussels, ta yi kira da a taimakawa Siriyawa miliyan 24 da dala biliyan 10.
Ofishin Kula da Aiyukan Jinkai, Babban Ofishin Kula da 'Yan Gudun Hijira da Shirin Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya ne suka fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka nemi da a kara yawan taimakon da ake baiwa miliyoyin Siriyawa.
Sanarwar ta ja hankali da cewa, lokaci na tafiya, kuma Siriyawa na kara fadawa cikin mawuyacin hali, kuma kasashe makotan Siriya sun karbi 4 daga cikin 5 na 'yan kasar a matsayin masu neman mafaka.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, Siriyawa da ke ciki da wajen Siriya da ke bukatar taimakon gaggawa sun tashi daga miliyan 20 zuwa miliyan 24 a wannan shekara ta 2021, kuma ana bukatar dala biliyan 10 don taimaka musu. Dala biliyan 4,2 a cikin Siriya, dala biliyan 5,8 kuma a kasashe makota da ke dauke da 'yan gudun hijirar Siriya.