Mutumin da ya kafa kamfanin Amazon na cinikayya a yanar gizo Jeff Bezos ya bayyana zai bai aikin da yake yi a ranar 5 ga watan Yuli. Zai kuma mika ragamar kamfanin ga Andy Jassy.
A yayin zaman masu ruwa da tsaki da suka zuba hannun jari a Amazon, Bezos ya sanar da zai bar aikin jagorantar Amazon daga ranar 5 ga Yuli inda Andy Jassy zai ci gaba da jagorantar kamfanin.
Bezos ya tunatar da cewa, a ranar 5 ga Yulin 1994 aka kafa kamfanin Amazon.
News Source: ()