Tsohuwar Ministar Kudi da Harkokin Waje ta Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta zama Shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
Sanarwar da aka fitar daga WTO ta ce, a zaman da majalisar zartarwar Kungiyar ta gudanar na musamman an amince da Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar ta Kungiyar.
Iweala ce mace ta farko kuma 'yar Afirka da ta zama Daraka Janar ta WTO, kuma za ta fara aiki a ranar 1 ga Maris inda za ta kammala a ranar 31 ga Agustan 2025.
Akwai rikicin kasuwanci a duniya da ke gaban sabuwar Daraktar. Ana bayyana cewar saboda yadda Iweala ta ke da kwarewa tare da mu'amala da kasashe manya da kanana, hakan zai sanya ta sake karfafa Kungiyar a duniya da dawo da martabarta da ta rushe a baya.
A gefe guda, Turkiyya ta bayyana gamsuwarta game da zabar Ngozi-Okonjo Iewala a matsayin Darakata Janar ta WTO.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar da cewa, "Muna taya murna ga Okonjo-Iweala da ke da kwarewar tattalin arziki da diplomasiyya. Muna fatan nasara a aiyukan da za ta yi a WTO."