Likitoci sun fara yajin aiki a Najeriya

Likitoci sun fara yajin aiki a Najeriya

Likitoci a Najeriya sun tafi yajin aikin sai baba-ta-gani sakamakon yadda aka gaza biyan su albashinsu.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi ya shaida cewa, ba su cimma matsaya ba a taron awanni 9 da suka gudanar da Ministan Kwadago da Aiyuka Chris Ngige.

Okhuaihesuyi ya ce, daga ranar Alhamis din nan sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

Okhuaihesuyi ya yi kira da gwamnati da ta biya albashin likitocin inda ya ce,

"Ba saboda likitoci kawai mu ke wannan yajin aikin ba, muna yi ne don dukka ma'aikatan lafiya. Ya kamata gwamnati ta sauke nauyin da ke kanta."

Likitocin na Najeriya sun baiwa gwamnati zuwa ranar 31 ga Maris don ta biya su albashinsu.

 


News Source:   ()