
Ma'aikata 14 sun bata a wata hanyar karkashin kasa da ake gina wadda ruwa ya fasa tare da shiga cikin ta.
Sashen agajin gaggawa na garin Zhuhai ya shaida cewa, jami'an ceto na ta kokarin tuntubar leburorin da ibtila'in ya rutsa da su.
Ana ci gaba da aiyukan ceto ba kakkautawa.
Sama da leburori dubu, motocin kwana-kwana 22 da injinan jan ruwa 5 ne suke aikin ceton.
Ana kuma binciken gano musabbabin kutsawar ruwa hanyar karkashin kasar.
News Source: ()