Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani karamin jirgin sama na musamman a kusa da garin Lille ne arewacin Faransa.
Jirgin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Bondues da ke Wambrechies inda ya fado jim kadan bayan tashin sa.
Mai koyar da tukin jirgin sama dan shekaru 31 da wani mai shekaru 75 sun rasa rayukansu.
An bayyana cewa, jirgin ya fado sakamakon matsala da ya samu.
News Source: ()