Kamfanin Xiaomi ya fara aiki a Istanbul

Kamfanin Xiaomi ya fara aiki a Istanbul

An buɗe masana'antar kamfanin fasaha na Xiaomi da takwaransa na Salcomp, wanda ke da damar samar da wayoyin hannu na zamani miliyan 5 a kowace shekara a Avcilar, Istanbul.

Mataimakin Ministan Sufuri da Lantarki, Omer Fatih Sayan a jawabin da ya gudanar a bukin bude masana'antar ya ce kamfanin Xiaomi a cikin shirin Turkiyya na da matukar muhimmanci.

Ya kara da cewa “Za mu yi farin ciki cewa mun shaida samar da wayoyin hannu miliyan 5 a kowace shekara a wannan cibiyar kuma a lokaci guda za a dauki mutane dubu 2 aiki. Ba wai kawai a fannin sarrafa kayayyaki ba, har ma a fannin bincike da ci gaba, muna sa rai kamfanin Xiaomi zai saka hannun jarin a cikin kasarmu.”


News Source:   ()