Kamfanin jiragen sama na RAM zai fara safara zuwa Antalya daga Kasabalanka

Kamfanin jiragen sama na RAM zai fara safara zuwa Antalya daga Kasabalanka

Kamfanin Jiragen Sama na Masarautar Morokko (RAM) zai fara safara kai tsaye daga garin Kasabalanka zuwa birnin Antalya na Turkiyya.

Shafin Facebook na Jiragen Sama na Masarautar Morokko ya sanar da cewa, daga ranar 11 ga Yuli zai fara safara kai tsaye daga filin tashi da saukar jiragen sama na Muhammad na Biyar da ke birnin Kasabalanka zuwa birnin Antalya na kasar Turkiyya.

Sanarwar ba ta bayar da bayanai game da nawa ne farashin tikitin safarar ba.

Safarar tsakanin Kasabalanka-Antalya za ta zama safara ta ka tsaye tsakanin Turkiyya da Morokko. A shekarar 2005 aka fara safara tsakanin Kasabalanka-Istanbul a shekarr 2019 kuma aka fara tsakanin Marakish-Istanbul.


News Source:   ()