Jirgin yai mara matuki mai suna AKINCI TIHA da kamfanin Baykar na Turkiyya ya samar ya kafa tarihi a sashen sufurin jiragen sama a kasar wajen tashi sosai.
Jirgin Bayraktar AKINCI TIHA ya yi tashin gwaji a Cibiyar Horo da Gwajin Tashin Jiragen Sama da ke Corlu inda ya yi nisan kafa dubu 38 da 39 a sama (Mita dubu 11,594).
Wannan e karo na farko da jirgi da aka samar a Turkiyya ya yi tashi zuwa sama kamar haka.
Jirgin Bayraktar AKINCI TIHA ya yi ta shawagi a sama har tsawon awanni 25 da mintuna 46.
News Source: ()