Jirgin ruwan jigilar fasinjoji na zamani na farko a duniya

Jirgin ruwan jigilar fasinjoji na zamani na farko a duniya

A shekarun 1800 aka fara safarar jiragen ruwa kanana na kasuwanci a tsakanin gabar tekunan Istanbul. A shekarun 1840 aka fara amfani da kwale-kwale masu inji don kaiwa da komowa a Istanbul. A shekarar 1830 kuma aka kafa kamfanin “Sharikatu Al-Khayriyya” inda aka kawo manyan jiragen ruwa don jigilar jama’a a tekun Istanbul. Daya daga cikin jagororin kamfanin Huseyin haki Efendi mutum ne mai son zamanantar da aiyuka da abubuwa ina tsawon lokaci ya dauka yana tunanin yadda za a zamanantar da safarar teku. Bayan aiyuka da yawa na tsawon shekara daya, sai suka samar da wani sabon tsari na jirgin ruwa mai iya zuwa gaba da baya. Sun aika da wannan bincike da suka yi zuwa masana’antar samar da jiragen ruwa ta Ingila. Ingilawa sun nuna kauna ga wannan zane na jirgin ruwa.

An dauki kusan shekaru 2 ana yin wannan aiki na samar da jirgin ruwa mai saukin amfani inda aka ba shi sunan “Suhulet”. A shekarar 1872 ya fara aiki tsakanin Uskudar da Kabatash kuma ya yi aiki na tsawon shekaru 89 a mashigar ruwa ta Istanbul.


 


News Source:   ()