Jirgin ruwan Turkiyya mai suna Fatih ya fara aiyukan neman albarkatun man fetur da iskar gas a rijiyar Amasra-1 da ke tekun Bahar Maliya.
Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa na Turkiyya Fatih DOnmez ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter.
A sanarwar da DOnmez ya fitar ya ce, "A Bahar Rum Fatih ya fara sabon aikin neman albarkatun mai da iskar gas a rijiyar Amasra-1. Tare da Addu'ar al'umarmu in sha Allah za a samu labari mai dadi."
News Source: ()