Jirgin ruwan dakon mai da ya taso daga tashar jiragen ruwa ta Freeport da ke Amurka dauke da ruwan man gas da ake kira "LNG Abalamabie" ya isa Turkiyya.
Bayanan da aka samu daga cibiyar bibiyar safarar jiragen ruwa ta kasa da kasa sun ce, jirgin ruwan ya taso daga Amurka a ranar 24 ga Janairu kuma ya isa tashar jiragen ruwa ta Aliaga da ke lardin Izmir da misalin karfe 08.22 na safiyar 10 ga Fabrairu.
Jirgin mai dauke da tutar Bermuda na dauke da LNG mitakyup dubu 170.
An kera jirgin a shekarar 2016.
News Source: ()