Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon karo da wani jirgin ruwan Rasha da jirgin ruwan masunta na Japan suka yi a gabar jihar Hokkaido ta Japan.
Lamarin ya afku a lokacin da jirgin ruwan na Rasha mai nauyin tan 662 mai suna "Amur" da ke dauke da ma'aikata 23 ya ci karo da jirgin ruwan masunta na Japan mai nauyin tan 9,7 a tashar jiragen ruwa ta Monbetsu.
Sakamakon hatsarin da ya afku a tekun Ohotsk, masunta 3 'yan kasar Japan sun mutu.
Tashar yada labarai ta Kasa ta Japan NHK ta bayyana cewa, Rundunar Sojin Ruwa ta Kasar ta aike da jirgin bayar da agaji da ceto.
News Source: ()