Jirage za su fara tashi zuwa kasashe daga sabon filin tashi da saukar jiragen saman Turkistan

Jirage za su fara tashi zuwa kasashe daga sabon filin tashi da saukar jiragen saman Turkistan

Sabon filin tashi da saukar jiragen saman Turkistan na kasar Kazakhstan da aka bude a ranar 1 ga watan Disamba zai fara sintirin jiragen sama a matakin kasa da kasa zuwa Istanbul a ranar 21 ga watan Maris.

Kamar yadda hukumar sararin samaniyyar kasar ta sanar sabon filin tashi da saukar jiragen saman Turkistan zai fara sintirin jiragen sama zuwa kasa da kasa.

Sanarwar ta kara da cewa filin tashi da saukar jiragen saman Turkistan da aka bude a ranar 1 ga watan Disamba zai fara sintirin jiragen saman tsakanin kasashe a ranar 21 ga watan Maris. 

Kanfanin jirgin saman Fly Arystan ne zai fara sintirin jiragen saman tsakanin Turkistan-Istanbul-Turkistan.

Jirgin zai fara sintirin ne sau biyu a sati daga bisani kuma ya kara zuwa sau bakwai. 

 

 

 


News Source:   ()