Jirage na ci gaba da zuwa sabon filin jirgin sama da aka gina a garin Fuzuli na Azabaijan, wanda aka kubutar daga mamayar Armeniya.
A cikin wata sanarwa da kamfanin jiragen sama na Azabaijan ya fitar, an bayyana cewa, jirgin "Airbus A340-500", mai mafi yawan daukar fasinja a cikin jiragen kamfanin, ya yi gwajin zuwa filin jirgin da ake ginawa.
An dauki 'yan jarida daga Baku babban birnin kasar zuwa Fuzuli ta jirgin sama mai suna "Karabakh" kuma tafiyar ta dauki kimanin mintuna 35.
Bugu da kari, an gudanar da tashin jirgin zuwa filin jirgin sama na Fuzuli tare da jirgin daukar kaya na "Boeing 747-400".
Da wannan jirgin, an kawo kaya zuwa Karabakh ta jirgin sama a karon farko.