Japan za ta taimakawa Musulman Arakan da dala miliyan 19

Japan za ta taimakawa Musulman Arakan da dala miliyan 19

Gwamnatin Japan ta ware dala miliyan 19 don sayen kayan abinci da na kula da lafiya ga Musulman Arakan 'yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a Bagaladash.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Japan ta fitar ta ce, za a bayar da taimako ga Musulman Arakan da suka gujewa zalunci da kisan kare dangin da ake musu a Myammar.

A karkashin shirin, za a baiwa Musulman na Arakan taimakon dala miliyan 19 ta hannun Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross da ke Japan, Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Kasa da Kasa.

Haka zalika, za a samar da kayan kula da lafiya a asibitoci 58 da ke Bangaladash, sannan za a raba kayan abinci ga 'yan gudun hijirar Arakan dubu 600 da ke kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akwai 'yan gudun hijirar Arakan kimanin dubu 900 a Bangaladash wadanda suka shiga kasar tun daga watan Agustan 2017.


News Source:   ()