Tun daga farkon shekarar 2021 zuwa yau, Isra'ila ta rushe gidajen Falasdinawa dubu 62.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Falasdin Fadi Al-Hadmi ya shaida cewa, daga farkon 2021 zuwa yau Isra'İla ta rushe gidajen Falasdinawa dubu 62.
Kamfanin dillancin labarai na Falasdin (WAFA) ya shaida cewa, Minista Hadmi ya karbi bakuncin Jakadan Jordan a Falasdin Muhammad Abu Wandi a gidansa.
A yayin ganawar, Hadmi ya bayyana har yanzu ana ci gaba da cusgunawa Falasdinawa tare da korar su daga gidajensu a unguwar Shaikh Jarrah, kuma akwai iyalai 86 da ke a unguwar Batn Al-Hawa da ke fuskantar barazanar kora daga gidajensu, akwai gidaje 100 a unguwar Silvan ta Gabashin Kudus na fuskantar barzanar rushewa.
Hadmi ya kara da cewa, daga farkon 2021 zuwa yau Isra'ila ta rushe gidajen Falasdinawa dubu 62.