Gwamnatin Isra'ila ta janye wasu dokoki da ta sanya a Zirin Gaza a lokacin da ta ke kai hare-hare a watan Mayu.
Sashen Aiyukan Gwamnati a Yankunan Falasdinawa (COGAT) ya shaida cewa, bayan sake duba zuwa ga yanayin da ake ciki, an bayar da izinin kamun kifi ga masuntan Zirin Gaza a nisan mil 15 a teku maimakon mil 12.
An bude kofar Karm Abu Salim da ke kan iyaka domin shiga da fitar da kayayyaki, an baiwa 'yan kasuwar Falasdin dubu 5 izinin shiga Isra'ila.
Hakan zai sanya a kara yawan ruwan shan da ake aikawa Gaza daga Isra'ila zuwa mitakyub miliyan 5.
News Source: ()