A Iran an kai farmaki kan cibiyoyin samar da kudin Kripto 147. A yayin farmakin an kwace nau'rorin kwamfuta guda dubu 1,300.
Tun daga watan Maris zuwa yau an gano wuraren samar da kudin Kripto sama da dubu 5 a Iran, an kuma kwace injina dubu 213 da ake yin aikin da su.
An gano an yi amfani da megawatt 606 wajen amfani da injinan da aka kwace.
Sakamakon matsalar katsewar lantarki, Iran ta hana aiyukan samar da kudin Kripto har sai bayan 22 ga Satumba.
News Source: ()