An bayyana cewa, Iran ta fara samar da alluran riga-kafin cutar Corona mai suna COVIRAN Barakat da ta kirkira kuma nan da karshen shekarar nan za a magance matsalar karancin allurar da ake fuskanta a kasar.
A yayin wani shiri da aka gudanar a Tehran, an yi gwajin COVIRAN Barakat kan masu sadaukar da kai a karo na 3 na gwajin ta.
An yi gwajin allurar a karo na 3 a kan Mamban Hukumar Yaki da Corona ta Kasa Minu Muhriz, Dan Majalisar Dokoki na yankin Sistan Balujistan Huseyin Ali Shehriyari da tsohon malamain makaranta Muhammad Ali Emirzerger.
Sanar da jagoran malaman kimiyya Muhamma Muhbir ya fitar ta ce, sun fara samar da allurar COVIRAN Barakat da yawa kuma nan da karshen shekarar nan za a magance matsalar karancin allurar da ake fuskanta a kasar.