An bayyana cewa, rundunar sojin Indiya ta gwada wani sabon makami mai linzami na zamani da zai iya daukar nukiliya da ta samar.
Jaridar Sputnik ta Rasha ta bayar da labarin cewa, Hukumar Binciken Tsaro da Habaka Aiyukan Soji ta Indiya (DRDO)ce ta samar da makamin mai suna "Agni P" wanda aka gwada shi da safiyar Litinin din nan a gabar tekun Bengal da ke Tsaunin Abdul Kalam.
An bayyana cewa, makamin "Agni P" da aka samar da dukkan fasahar zamani ya samu nasarar gwajin da aka yi.
Makamin mai linzami da ake iya sarrafa shi daga nesa na iya daukar bam din nukiliya mai iya yin tafiyar kilomita dubu 1 zuwa dubu 2 a sama.