IMF: Corona za ta jefa mutane miliyan 32 cikin bakin talauci a Afirka

IMF: Corona za ta jefa mutane miliyan 32 cikin bakin talauci a Afirka

Asusun Bayar da Lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, annobar Corona (Covid-19) da ta ke illata tattalin arzikin kasashe, za ta jefa mutane miliyan 32 cikin bakin talauci a yankin Saharar Afirka.

A rahoton da Asusun na IMF ya fitar game da tattalin arzikin kasashen da ke yankin Saharar Afirka an bayyana cewa, allurar riga-kafin da ake yi za ta kara yawan kudaden da kasashen su ke kashewa da kaso 50 cikin dari.

Rahoton ya ce, yankin na Saharar Afirka ne zai zama mafi koma baya wajen cigaba a duniya a shekarar 2021, raguwar habakar da aka samu na kaso 1,9 a shekarar da ta gabata, a wannan shekarar an yi hasashen za ta kasance kaso 3,4.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, sakamakon halin da aka shiga, adadin masu fama da bakin talauci a yankin zai kai mutane miliyan 32, kuma a kasashe da dama har nan da shekarar 2025 kudaden da mutane suke samu ba zai dawo kamar yadda ya ke kafin bullar cutar ta Corona ba.

A yankin da aka samu rasa rayuka dubu 117 sakamakon Corona, jimillar mutane miliyan 4,4 cutar takama.

 

 


News Source:   ()