Wani jirgin kasa na dakon kaya ya sauka daga layin dogo a jihar Iowa ta Amurka inda ya kone kurmus.
Har yanzu ba a san musabbabin kaucewar jirgin kasan dakon kaya daga kan layin dogon na Amurka ba.
Jirgin ya kama da wuta bayan hatsarin. An bayyana cewa, jirgin na dauke da kayan fashewa na takin zamani da sinadarin amoniyom.
Ba a bayyana ko an samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon hatsarin.
'Yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar da ta kama, an kuma kwashe jama'ar yankin daga gidajensu.
News Source: ()