Hatsari a mahakar ma'adanai a Gana

Hatsari a mahakar ma'adanai a Gana

Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin da ya afku a wata mahakar ma'adanan zinare a yankin Upper West na Gana.

Ministan Yankin Upper West Stephen Yakubu ya shaida cewa, sakamakon mamakon ruwan sama mahakar ma'adanan zinare a ba ta bisa ka'ida a garinTalensi ta rufta.

Yakubu ya kara da cewa, an gano gawarwakin mutane 9 a karkashin mahakar ma'adanan, an kuma kubutar da mutum 1 da ransa.

Ana ci gaba da aiyukan ceto a yankin.

 


News Source:   ()