Hatsari a mahakar ma'adanai a Afganistan

Hatsari a mahakar ma'adanai a Afganistan

Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar kasa a wata mahakar ma'adanan zinare da ke jihar Badahshan din arewa maso-gabashin Afganistan.

Kakakin helkwatar 'yan sandan Badahshan, Sanaullah Ruhani ya shaida cewa, sakamakon dusar kankara da mamakon ruwan sama, mahakar ma'adanan zinare da ke gundumar Rajistan ta rufta inda leburori 4 suka mutu, wasu 3 kuma suka jikkata.

A kowacce shekara mutane da dama na mutuwa a Afganistan sakamakon hadurran da ake samu a mahakar ma'adanai saboda rashin daukar matakan kariya yadda ya kamata.


News Source:   ()