Daraktan Hukumar Kididdigar Kasa da Kasa ta Fitch Ratings, Douglas Winslow ya bayyana cewar ana sa ran hauhawar farashi a Turkiyya zai ragu da kashi 11 cikin 100 a karshen shekarar 2021.
Hukumar Fitch Ratings ta bayyana hakan a taron karawa juna sani da aka gudanar ta hanyar sadarwa ta bidiyo mai taken "Turkiyya da Cibiyoyin Kuɗi".
Da yake jawabi a taron na karawa juna sani, Daraktan Hukumar Douglas Winslow ya ce,
"Muna sa ran hauhawar farashi zai ragu da kashi 11 cikin 100 a karshen wannan shekarar kuma zuwa kashi 9.2 a karshen shekarar 2022. Wannan har yanzu yana sama da kididdigar Babban Bankin Jumhuriyar Turkiyya (CBRT)."