Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa na shirin saka hannun jari a Turkiyya.
Erdogan ya tarbi mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Tahnoun bin Zayed Al Nahyan, wanda ke Ankara babban birnin kasar.
A cewar sanarwar da Daraktar Sadarwa ta Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ya fitar, a yayin ganawar, an tattauna dangantakar kasashen biyu da batutuwan da suka shafi yankin, sannan an tattauna batun saka hannun jarin Hadaddiyar Daular Larabawa a Turkiyya.
Daga baya a wani shirin talabijin da Erdogan ya halarta ya bayyana cewa,
"Suna da mahimman manufofin saka hannun jari da tsare -tsaren saka hannun jari. Na yi imanin Hadaddiyar Daular Larabawa za ta sanya hannun jari mai mahimmanci a cikin kasarmu cikin kankanin lokaci."