Hadaddiyar Daular Larabawa za ta saukar da ruwan sama ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka na musamman da aka samar, wadanda za su dinga yawo a cikin gaji-mare.
Kamfanin dillancin labaraina Sputnik ya labarta cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa ta shirya amfani da jiragen sama marasa matuka wajen yin diri da girgiza a cikin gaji-mare inda za ta kara yawan ruwan saman da ake yi a kasar.
Shugaba shirin ruwan saman Alya Al-Muzrui ya shaida cewa, jiragen saman marasa matuki da za su tashi sama za su sauya karfin lantarkin da ke gaji-mare.
Al-Muzrui ya kara da cewa, a Ingila aka samar da jiragen, kuma an gwada amfani da su a Dubai.
Jami'in ya ce, duk da yawan gaji-mare da ake da shi a kasar amma ana fuskantar fari.
A shekarar 2017 Hadaddiyar Daular Larabawa da ke fama da karancin ruwan sama, ta ware dala miliyan 15 don gudanar da aiyuka 9 na kyautata samun ruwan sama.
Idan aka samu nasarar shirin, to masana na cewa za a iya amfani da manyan jiragen sama wajen yin aiki.