Gyadar Antep mashahuriya a Turkiyya

Gyadar Antep mashahuriya a Turkiyya

Idan aka ambaci garin Gaziantep dake kudu maso-gabashin Turkiyya abu na farko da yake fara zuwa kwakwalen mutane shi ne, gyadar Antep da ta yi shuhura a ciki da wajen Turkiyya. Sakamakon yadda aka fara kafa kamfanin sarrafa gyada a Turkiyya a Gaziantep, na nufin wannan gyada da asalinta ya fito daga Tsakiyar Asiya. Sabuwar gyadar Antep da aka shuka tana fara bayar da ‘ya’ya bayan shekaru 10. Kowacce bishiya tana bayar da kusan kilogram 10. Kuma tana yin yin shekaru 100 zuwa 150 kafin ta mutu.

Ana cin gyadar Antep zalla kuma ana amfani da ita wajen samar da kayan zaki, tana da sinadaran gina jiki da yawa tare da kunsar sinadarai da dama. An san ta da tsaftace huhu. Tana sanya kirji ya yi laushi, tana tausasa ciwuka tare da taimakawa wajen warkar da ciwon tari. Tana taimakawa wajen narkar da man da ke cikin jini wanda hakan ke rage hatsarin kamuwa da ciwukan zuciya. Tana dauke da sinadarin Vitamin B6 wanda ke taimakawa wajen magance ciwukan daji daban-daban da kuma bayar da garkuwa daga cututtuka da yawa. Gyadar Antep na dauke da nau’ikan abinci da jikin dan adam yake bukata, a saboda haka ake kiranta “Abincin da Ya Hada Komai”.


News Source:   ()