Gwamnatin Amurka ta amince da a sayarwa da Taiwan makamai

Gwamnatin Amurka ta amince da a sayarwa da Taiwan makamai

Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Joe Biden ta amince da a sayarwa da Taiwan makamai har na dala miliyan 750.

Labaran da Bloomberg ta fitar na cewa, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da Majalisar Dokoki game da sayar da makaman.

Yarjejeniyar sayar da makaman da gwamnatin Biden ta amince da ita, ta tanadi sayar da igwa guda 40 da setin kayan harbi dubu 1700.

Ana tunanin wannan mataki zai bakantawa China da ta ke kallon Taiwan a matsayin wani bangaren nata.


News Source:   ()