Guguwar Nora ta kunna kai Mekziko

Guguwar Nora ta kunna kai Mekziko

Guguwar Nora da ke gudun kilomita 130 a awa 1 ta kunna kai arewa maso-yammacin Mekziko inda ta janyo iska mai karfi da mamakon ruwan sama.

Guguwar ta Nora da ke a maki na 1 wajen hatsari, na ci gaba da gudu zuwa kudu maso-yammacin Jalisco da ihar Baja Californa.

Mahukunta sun bayyana cewa, sakamakon iska mai karfi da mamakon ruwan sama, ruwa ya mamaye yankuna da dama, ana ci gaba aiyukan kwashe jama'a daga yankunan.

A ranar 22 ga Agusta ma guguwar Grace ta kunna kai jihohin Veracruz da Grace inda mutane 11 suka rasa rayukansu.

A lokacin bazara ana yawan samu guguwa mai karfi a yankin da kasar Mekziko ta ke. Guguwowin na yawan zama a matakin hatsari na 2 da na 3.


News Source:   ()