Guguwar Henri da ta faro daga Tekun Maliya kuma ta ke a mataki na 1 kuma mai gudun kilomita 120 a awa 1 ta kunna kai zuwa gabashin Amurka.
Hukumar Kula da Guguwa ta Amurka ta ce, guguwar ta kara karfi sosai tare da fara yin barazana.
Ana sa ran guguwar za ta tunkari arewa maso-gabashin Amurka, kuma mahukuntan kasar sun yin gargadi kan yiwuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankunan New York, Long Island da New England.
An kuma sake yin gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa da katsewar lantarki.
News Source: ()