A tsakanin watannin Nuwamban 2020 da Yulin 2021 fitar da man zaitun daga Turkiyya zuwa kasashen waje ya karu da kaso 6 wanda ya kama dala miliyan 96.
Shugaban Kungiyar Masu Noma da Fitar da Man Zaitun zuwa Kasashen Waje na yankin Aegean Davut Er ya shaida cewa,
"A tsakanin 1 ga Satumban 2020 da 31 ga Yulin 2021 an samu karin kaso 1,6 na man zaitun din da ake cin abinci da shi wanda ya kama na dala miliyan 125. A tsakanin 1 ga Nuwamban 2020 da Yulin 2021 kuma fitar da man zaitun din ya karu da kaso 6 wanda ya kama na dala miliyan 96."
Davut Er ya ci gaba da cewa, Amurka ce a kan gaba wajen sayen man zaitun daga Turkiyya da ta sayi na dala miliyan 33, Jamus kuma ke kan gaba wajen sayen na ci a abinci da dala miliyan 36.