Fitar da madara da kayayyakin da ake samarwa da ita daga Turkiyya zuwa China na kara habaka inda ya kai na dala miliyan 9,3 a watanni 2 na farkon 2021.
Sakamakon aiyukan hadin gwiwa da Ma'aikatar Kasuwanci da Ma'aikatar Noma da Gandun Daji na Turkiyya, an gaggauta kai madara zuwa China tun bayan da aka janye dokar hana yin hakan a watan Mayun shekarar da ta gabata.
A watanni 7 na 2020 an kai madara da dangoginta zuwa China na dala miliyan 14,6.
'Yan kasuwa da ke son zama a kasar sun kara habaka aiyukan tallata kayayyakinsu ta hanyar hadin kai.
A tsakanin watan Janairu da Fabrairu an fitar da madara ta dala miliyan 9,3 zuwa China daga Turkiyya.