Fitar da madara da dangoginta daga Turkiyya zuwa kasashen waje ya karunda kaso 12 a watanni 3 na farkon 2021 idan aka kwatanta da watanni 3 na farkon 2020. China ce a kan gaba da aka kai mata kayan dala miliyan 17,2.
Bayan janye dokar hana kaiwa China kayayyaki a shekarar da ta gabata, fitar da kayayyaki zuwa kasar ya samu habaka.
A watanni 3 na farkon shekarar 2020 an kai madara da dangoginta zuwa kasashen waje na dala miliyan 71 da dubu 560 inda a watanni 3 na farkon 2021 kuma aka fitar da na dala miliyan 80 da dubu 180. Fitar da madarar zuwa kasashen waje ya karu da kaso 12,4.
China ce a kan gaba wajen karbar madara da dangoginta daga Turkiyya.
A shekarar 2020 an kai madara da dangoginta na dala miliyan 14 da dubu 596 zuwa China inda a 2021 kuma aka fitar da na dala miliyan 17 da dubu 243.