Fitar da kofunan gilasai ya wuce na dala biliyan 2.4 a cikin farkon watanni 5 na shekara tare da ƙaruwar kaso 54.1 bisa ɗari idan aka kwatanta da na daidai lokacin a 2020.
Dangane da bayanan kungiyar kofunan tangaran (Glassware), ta fitar, hadi da kayan tebur da na kicin an fitar da na dala biliyan 2 da miliyan 409 a cikin watan Janairu zuwa Mayu.
An ga adadin da aka fitar mafi girma a watan Maris tare da na dala miliyan 565.1, sai kuma a Afrilu da dala miliyan 553.4 da Mayu da dala miliyan 465.
Fitar da kaya a cikin watan Mayu ya karu da kashi 86 cikin dari idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata kuma ya kai dala miliyan 465.
Kashi 51 cikin dari na fitarwa an yi su zuwa ƙasashen Turai. Kasar Birtaniya ce ta fi sayen kayayyakin.