Fitar da keken da Turkiyya ke yi ya haura dala miliyan 70 a cikin watanni 6 na wannan shekarar, wanda ya karu da kashi 88 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Kekunan Turkiyya ana buktarsu musamman a kasashen Turai. Fitar da kekuna, wanda ya kai na dala miliyan 37.2 a cikin watan Janairu zuwa Yuni na bara, ya karu zuwa dala miliyan 70 a daidai wannan shekarar. Yawan karuwar fitar da kaya ya kai kashi 88 cikin dari.
An fitar da kekuna zuwa kasashe 92 daga Turkiyya. Jamus ta kasance ta farko tare da fitar da dala miliyan 10.2. Finland ta biyo bayanta da dala miliyan 9.8 sai Faransa da dala miliyan 9.3.