An samu bunkasar fitar da kayayyaki daga kasar Turkiyya zuwa kasashen waje a cikin watan febrairu da karin kaso 9.6 cikin dari wanda ya kai na zunzurutun kudi har dala biliyan 16 da miliyan 12.
Kasar Jamus ce ta fi sayen kayayyaki daga Turkiyya a watan jiya, idan aka kwatanta da kayayyakin da Jamus ta saye daga Turkiyya a watan Febrairun bara a bana an samu kari daga dala miliyan 164 da dubu 11 zuwa biliyan 1 da miliyan 359 da dubu 318.
Daga cikin kasashen da suka fi sayen kayayyakin Turkiyya sun hada da Amurka, China, Birtaniya da Faransa.
Haka kuma zuwa kasar Amurka an fitar da kayayyaki da karin dala miliyan 160 da dubu 412 inda a jumalace a wannan karon aka fitar da kayayyakin zuwa kasar har na dala miliyan 823 da dubu 542, zuwa China kuma an samu karin fitar da na dala miliyan 109 da dubu 132, a jumlace an fitar da na dala miliyan 252 da dubu 346, na Ingila kuma an samu karin dala miliyan 104 da dubu 108 inda a jumlace aka fitar da na dala miliyan 931 da dubu 835, zuwa Faransa kuwa na samu karin fitar da kayayyakin na dala miliyan 83 da dubu 49 a jumlace an fitar da na dala miliyan 685 da dubu 372.