Fitar da kayayyaki daga Turkiyya ya karu a watan Janairu

Fitar da kayayyaki daga Turkiyya ya karu a watan Janairu

Ministan kasuwancin kasar Turkiyya Ruhsar Pekcan ta sanar da cewa kasar Turkiyya ta fitar da kayayyaki masu dinbin yawa zuwa kasashen ketare a cikin watan Janairu wanda ba a taba samun hakan ba a cikin watan.

Dangane ga alkaluman harkokin fitar da kayayyaki na watan Janairun 2021 "Idan aka kwatanta da na shekarar bara a watan Janairun bana an samu karin fitar da kayayyaki da kaso 2.5 cikin dari wanda ya kai na kudi dala biliyan 15 da miliyan 48"

Pekcan, ta kara da cewa duk da matsalolin kai-kawo da annobar Korona virus ke ci gaba da haifarwa a doron kasa kasar Turkiyya na ci gaba da samun bunkasa a fannoni da dama.

 


News Source:   ()