A tsakanin watan Janairu da Yunin 2020, an fitar da kayan marmari da kayan miya daga Turkiyya zuwa kasashen waje na dala miliyan 777.
Wannan adadi ya karu da kaso 20 a irin wannan lokaci a shekarar 2021 da ake fama da cutar Corona inda ya tashi zuwa dala miliyan 936.
Jamus a kan gaba wajen sayen kayan marmari da na miya da aka kai zuwa kasashen waje sama da 100 daga Turkiyya, inda ta sayi na dala miliyan 133.
Amurka ce ta biyu wadda aka kaiwa kayan dala miliyan 114.
A wannan lokaci dai na watanni 6 an kai kayan marmari da na miya na dala miliyan 83 zuwa kasar Iraki da ke makotaka da Turkiyya.