Fitar da furenni daga Turkiyya na karuwa

Fitar da furenni daga Turkiyya na karuwa

A tsakanin 1 ga Janairu da 21 ga Fabrairun 2021, an samu karin kaso 19 na furennin da Turkiyya ke fitarwa kasashen waje idan aka kwatanta da na lokacin a shekarar da ta gabata.

A tsakanin 1 ga Janairu da 21 ga Fabrairun 2020 an fitar da furenni na dala miliya 19 da dubu 953 zuwa kasashen waje daga Turkiyya. A wannan shekarar kuma an fitar da na dala miliyan 23 da dubu 752.

Turkiyya da ke da nau'ikan furenni sama da dubu 3,500, ana fitar da mafi yawan su zuwa kasashen waje.

Ana kai furennin zuwa kasashe 83 da suka hada da na Turai.

 


News Source:   ()